Yan Bindiga Sun Tare Amarya Da Kawayenta Ranar Daurin Aure a Jihar Neja.

Ƴan bindiga sun yi ƙokarin sace wata amarya tare da ƙawayenta suna kan hanyarsu ta sada ta da gidan miji.

Amaryar dai ta yi ta maza ta tube rigar amarci inda ta ranta ana kare cikin daji domin tsira daga faɗa wa hannun ƴan bindigan.

Ƴan bindigan sun sace biyu daga cikin ƙawayen amaryar amma sun samu sun kuɓuta daga hannun miyagun daga baya.

Jihar Neja – Wata amarya a jihar Neja ta sha da ƙyar lokacin da ƴan bindiga suka kai musu farmaki ita da ƙawayenta ana kan hanyar kai ta gidan miji.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa amaryar ta tuɓe rigar amarcinta inda ta ranta ana kare ta yi tafiya mai nisa a cikin daji domin tserewa daga shiga hannun ƴan bindigan.

Amaryar dai an ɗauko ta ne daga wani ƙauye cikin ƙaramar hukumar Paikoro zuwa Kuta, hedikwatar ƙaramar hukumar Shiroro, lokacin da ƴan bindigan suka kai musu farmaki a kusa da Kaffin-Koro cikin ƙaramar hukumar Paikoro.

Wata ƴar uwar amaryar wacce ta nemi da a sakaya sunanta, ta bayyana cewa suna cikin tsaka da tafiya ne kawai kafin su ankara sai ƴan bindigan suka kawo musu hari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
X
DANNA NAN KAGA BIDIYAN 👈😭💣🇳🇪🇳🇬