Yadda Jami’an Tsaro Suka Halaka ‘Yan Bindiga Biyar a Jihar Katsina Bayan Sun Kai sumame.

Jami’an tsaro sun samu nasarar kai samame a maɓoyar ƴan bindiga tare da sheƙe biyar daga cikinsu a jihar Katsina.

Tawagar jami’an tsaro wacce ta ƙunshi ƴan sanda da ƴan sakai tare da mafarauta ta kai samamen ne a ƙananan hukumomin Batsari da Jibia.

Tawagar jami’an tsaron ta kuma samu nasarar cafke ɗaya daga cikin shugabannin ƴan bindiga da ya addabi yankin.

Jami’an ƴan sanda tare da haɗin guiwar ƴan sakai da mafarauta sun halaka ƴan bindiga biyar da cafke ɗaya daga cikin shugabanninsu a jihar Katsina.

Jami’an tsaron sun samu wannan nasarar ne lokacin da suka kai samame ranar Asabar a maɓoyar ƴan bindigan da je a ƙananan hukumomin Batsari da Jibia a jihar Katsina, cewar rahoton Vanguard.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Abubakar Sadiq, a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, ya bayyana cewa jami’an rundunar na tawagar hana garkuwa da mutane da na sashin bincike na musamman ne suka jagoranci kai samamen.

A cewar Sadiq, tawagar jami’an ta tarwatsa maɓoyar ƴan bindiga da dama a ƙauyukan Marake, Garin Yara, da Garin Labo, dukkansu a ƙaramar hukumar Batsari.

Haka kuma tawagar jami’an ta kai samame tare da tarwatsa maɓoyar wani ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga, Audu Lankai, wanda ya addabi ƙaramar hukumar Jibia da maƙwabtanta.

Sadiq wanda ya bayyana sunan ɗan ta’addan da aka cafke a matsayin Abubakar Idris, ya bayyana cewa an ƙwato shanu 38, tumakai 40 da awakai 65 a yayin samamen, rahoton Channels tv ya tabbatar.

A cewar kakakin rundunar ƴan sandan jami’ansu na ci gaba da zagaya yankin domin cafke sauran ƴan bindigan da ƙwato kayayyakin da ke hannunsu yayin da ake ci gaba da bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
X
DANNA NAN KAGA BIDIYAN 👈😭💣🇳🇪🇳🇬