Yadda Yan Bindiga Suka Kaiwa Sarki A Fadar Da Mummunan Hari.

A daren Talata aka samu wasu miyagu dauke da bindigogi, sun sace Sarkin Oghara a jihar Kogi.

. Dann Hoton Nan πŸ‘†πŸ‘†πŸ‘†

Ana zargin β€˜yan bindigan sun yi garkuwa da Basaraken ne domin su samu kudin fansa a kansa.

Harin ya yi sanadiyyar wata mai aiki a fadar Sarkin, sannan an hada da wasu Dattawa an dauke.

Mai rike da sarautar kasar Oghara a karamar hukumar Kabba Bunu ta jihar Kogi, yana hannun β€˜yan bindiga a yanzu da ake tattara rahoton nan.

Wani labari mara dadi da ya fara fitowa a Daily Trust, ya tabbatar da cewa β€˜yan bindiga sun je fadar Basaraken a tsakar daren Talata, suka yi gaba da shi.

A wajen wannan mugun hari, an rasa wata daga cikin ma’aikatan Sarkin. An tabbatar da mutuwar Toyin Onare wanda miyagun suka budawa wuta.

a wajen wannan mugun hari, an rasa wata daga cikin ma’aikatan sarkin. an tabbatar da mutuwar toyin onare wanda miyagun suka budawa wuta.

Rahoton ya ce baya ga Mai martaban da aka yi nasarar daukewa, β€˜yan bindigan sun tsere da wasu Dattawa biyu; Pa David Obadofin da Cif Temidayo Elewa.

Kakakin β€˜yan sanda na reshen Kogi, SP William Aya ya tabbatar da haka ga manema labarai.

William Aya yake cewa da kimanin karfe 3:00 na dare wadannan miyagu suka shigo fadar Basaraken, su ka shiga harbe-harbe ko ta ina, kafin suyi ta’adin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
X
DANNA NAN KAGA BIDIYAN πŸ‘ˆπŸ˜­πŸ’£πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡¬