Tofa! Yadda Tubabben Dan Boko Haram Ya Kitsa Farmaki Kan Sojoji, 3 Sun Mutu, 4 Sun Jikkata.

Tofa! Yadda Tubabben Dan Boko Haram Ya Kitsa Farmaki Kan Sojoji, 3 Sun Mutu, 4 Sun Jikkata.

Danna Hoton nan πŸ‘†πŸ‘†πŸ‘†

innalillahi: Sojojin Najeriya sun kama wani rikakken tsohon dan Boko Haram da ake zargi da hada kai da tsoffin abokansa.

Rahoto ya bayyana yadda wannan dan ta’adda ya mika wuya a baya, amma yake kitsa hari kan sojoji.

Tun farko, ana ci gaba da dasa ayar tambaya game da sahihancin tuban β€˜yan ta’addan Boko Haram.

Borno, Najeriya – Jami’an rundunar Operation Hadin Kai sun titsiye wani mai suna Ba’ana Bdiya da aka ce tubabben dan ta’addan Boko Haram ne bisa zargin hannu a dasa wani bam da ya yi sanadiyyar mutuwar wasu sojoji.

Kafar labaran tsaro ta Zagazola Makama ta ruwaito cewa, wanda ake zargin da aka fi sani da Manci ya ba da bayanai ne ga β€˜yan ta’addan a ranar 16 ga watan Maris kan motsin sojoji.

Majiya ta bayyana cewa, bayanan sirri da Manci ya bayar ne ya kai ga yiwa sojoji kwanton bauna tare da tashin wasu daga cikinsu da bama-bamai IED.

Rahoton da Legit.ng Hausa ta samo daga jaridar TheCable na cewa, sojoji uku ne suka rasu, inda wasu hudu suka samu munanan raunuka a yankin Banki da ke jihar Borno.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
X
DANNA NAN KAGA BIDIYAN πŸ‘ˆπŸ˜­πŸ’£πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡¬