INNA LILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN: An Shiga har gida sun yi wa ‘yar dan majalisar dokokin jihar Borno kisan gilla…

Wasu da ba a san ko su wanene ba sun shiga har gida sun yi wa ‘yar dan majalisar dokokin jihar Borno mai wakiltar Ngala, Honarabul Bukar Abacha kisan gilla a daren jiya a garin Maiduguri, jihar Borno..

Rariya ta gano cewa lamarin, wanda ya auku bayan sallar isha’i.

Bayan dawowa daga sallar isha’i, mijin mamaciyar mai suna Ammabuwa, ya zo ya tarar da gawar ta ne kwance, inda hannuwanta da kafafuwanta suke a daure, yayin da kuma dan su mai shekaru biyu yana gefe yana kuka.

Daga nan mijin ya dauki gawar ya garzaya ofishin ‘yan sanda reshen Gwange, inda daga nan aka wuce da ita asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri domin gudanar da bincike.

Har zuwa yanzu dai jami’an ‘yan sanda ba su fitar da sakamakon binciken na su ba game da ko su wa ake zargi da yin kisan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
X
DANNA NAN KAGA BIDIYAN 👈😭💣🇳🇪🇳🇬