Rashin Tausayi: An Kama Wani Matashi da Ake Zargin Ya Halaka Mahaifinsa Kan Abu 1 a Arewa.

Yan sanda sun kama wani matashi Ι—an shekara 29 a duniya bisa zargin ya halaka mahaifinsa a Jos, babban birnin jihar Filato.

Rahoto ya nuna matashin mai suna, Joseph Yake, ya Ι—auki taΙ“arya ya maka wa mahaifinsa a kai bayan sun samu wani Ι—an saΙ“ani.

Kwamishinan Ζ΄an sandan Filato, Hassan Steve Yabanet, ya ce da zaran sun gama bincike kan lamarin, zasu gurfanar da wanda ake zargi a gaban Ζ™uliya.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta tattaro, Ζ΄an sandan sun kama matashin ne bisa zargin ya buga wa mahaifinsa taΙ“arya, kuma daga karshe rai ya yi halinsa.

Kwamishinan Ζ΄an sandan jihar Filato, Hassan Steve Yabanet, ne ya bayyana haka yayin da yake nuna wanda ake zargin a hedkwatar Ζ΄an sanda ranar Talata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
X
DANNA NAN KAGA BIDIYAN πŸ‘ˆπŸ˜­πŸ’£πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡¬