Innalillahi wainna ilaihirrajiun Dalibar Ajin Karshe a Jami’ar Usman Danfodio ta rasu tare da ‘Yar ta a Hatsarin Mota.

Innalillhi wa inna ilaihi raji’un: Yanzu muka sami wani labari daga shafin Hausaloaded kamar yadda suma suka samo labarin daga shafin Dailynigerian, inda suka wallafa labarin wata mata mai suna Sha’awanatu.

👇👇👇👇👇👇

Ga dai yadda suka wallafa labarin kamar haka.

Sha’awanatu na tafiya hutun sabuwar shekara tare da mijinta a lokacin da ta samu hatsarin mota a ranar 23 ga Disamba, 2021 a kan hanyar Talata Marafa- Gusau, kan hanyar zuwa gidanta da ke Zariya daga jami’arta da ke Sakkwato.

Hadarin ya yi sanadiyar mutuwar diyarta Khadijah mai shekaru uku da haihuwa kuma Sha’awanatu ta samu rauni a ciki da kuma ta jiki.

Sha’awanatu Imran ta rasu ne a daren ranar Asabar da ta gabata da misalin karfe 9:17 na dare bayan ta shafe kwanaki 36 tana jinya a asibitin Shika Zaria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
X
DANNA NAN KAGA BIDIYAN 👈😭💣🇳🇪🇳🇬