An daure wata mata mai shayarwa bisa laifin satar indomie
Babbar Kotun Tarayya da ke Ado Ekiti ta yanke hukuncin daurin shekaru hudu ga wata uwa mai shayarwa, mai suna Yinka Akinwande, bisa samun ta da laifin satar taliyar indomie da kuษin ta ya kai kimanin Naira miliyan 5.5.
Danna nan Ka ga ๐๐๐๐
A cewar bayanan tuhumar, wacce ake tuhumar โtsakanin watan Agustan 2015 zuwa Oktoba 2019 a sashin shariโa na Ado-Ekiti ta aikata laifin damfara ta hanyar karษar kaya (indomie) daga hannun wani Bolanle Akarakiri .โ Jaridar Daily Nigerian Hausa na ruwaito
Dan sanda mai shigar da kara, Samson Osobu, wanda ya ce wacce ake kara ta aikata laifin ne a lokacin da take wakiliyar tallace-tallacen mai karar, ta kira tare da gabatar da kayan a hannun shaidu guda biyu: wanda ya shigar da karar da kuma jamiโin โyan sanda mai bincike, John Olotu.
Lauyan da ke kare mai wa ce a ke ฦara, R.A. Mohammed, ya roki kotun da ta yi wa wacce ake ฦara sassauci, inda ta ce wacce take karewa uwa ce mai shayarwa da jariri dan wata hudu.
Mai shariโa Babs Kuewumi ya ce ya yi laโakari da rokon jinkai da lauyan ya yi.
โDaga shaidar da mai gabatar da kara ya tabbatar, kotu ta samu wacce ake kara da laifi kamar yadda ake tuhumar ta. A nan na yanke wa wacce a ke tuhuma hukuncin zaman gidan yari na shekaru hudu,โ in ji alฦalin.