Boko Haram sun kashe manoma 40 a hare-hare daban-daban a Yobe.

Danna Nan πŸ‘†πŸ‘†πŸ‘†πŸ‘†

Wasu da ake zargin mayakan kungiyar Boko Haram ne sun kashe manoma kusan 40 a kauyen Gurokaya da ke karamar hukumar Gaidam a jihar Yobe.

A cewar rahoton da jaridar Punch ta fitar, an kashe manoman ne a wasu hare-hare da maharan suka kai a tsakanin ranakun Litinin zuwa Talata.

Mazauna yankin da su ka zanta da jaridar sun danganta kashe-kashen da gazawar manoman yankin wajen biyan haraji ga Ζ΄an ta’addan a lokacin girbin su.

β€œβ€™Yan ta’addan sun kai farmaki kauyen ne da misalin karfe 5 na yamma da karfe 6 na yamma, suka kira mazauna garin, suka tattara su a bayan gari, suka bude musu wuta,” kamar yadda wani dan yankin ya shaida wa wakilin jaridar ta wayar tarho a ranar Laraba.

β€œSama da mutane 17 ne su ka mutu nan take ranar Litinin. Sauran kimanin 20 na daga cikin wadanda su ka taho daga Gaidam da kauyukan da ke makwabtaka da kauyen da lamarin ya shafa domin binne mutum 20 na farko, ranar Talata.

β€œLokacin da su ke komawa gida, motarsu ta bi ta kan wani bam da maharan suka binne; 10 sun mutu nan take, kuma kusan 10 sun mutu a cibiyar kula da lafiya a matakin farko na Gaidam, inda aka garzaya da su bayan harin.”

A halin da ake ciki, kakakin rundunar β€˜yan sandan jihar Yobe, Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da faruwar hare-haren.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
X
DANNA NAN KAGA BIDIYAN πŸ‘ˆπŸ˜­πŸ’£πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡¬