Yan Bindiga Sun Sace Mutane da Yawa a Kano Ƙaramar Hukumar Jihar.

Yan bindiga sun kashe mutane sun yi garkuwa da wasu da ba a tantance yawansu ba a karamar hukumar Ƙaraye ta jihar Kano.

Mazauna ƙauyuna Yola da abun ya faru sun ce maharan sun kai hari a jere, sun tafka ta’asa tun daga ranar Asabar da ta wuce.

Ƙaraye da Rogo na fuskantar barazanar hare-haren ‘yan bindiga saboda kusancin Rogo da jihohin Kaduna da Katsina.

Kano – Rahotanni sun bayyana cewa har yanzun ba a tantance yawan mutanen da yan bindiga suka sace da waɗanda suka kashe ba a ƙauyen Yola, ƙaramar hukumar Ƙaraye a jihar Kano.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta tattaro, hakan ya faru ne bayan jerin hare-haren da ‘yan bindigar suka kai ƙauyen a baya-bayan nan.

Wani mazaunin garin wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda tsaro ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar a lokuta daban-daban a kauyen.

Ya bayyana cewa ba zai iya tantance yawan mutanen da aka sace ko aka kashe ba yayin harin.

“Na samu labarin cewa a harin farko da aka kai, an yi garkuwa da mutane kusan hudu, aka kashe biyu yayin da a hari na biyu an sace mutane biyu sannan aka kashe daya.”

“A zahirin gaskiya yanzun ƙaraye na buƙatar a girke mata dakarun sojoji saboda irin waɗan nan hare-hare.”

An tattaro cewa a baya-bayan nan, yankin kananan hukumomin Karaye da Rogo na Kano na fuskantar barazanar rashin tsaro saboda kusancin Rogo da jihohin Katsina da Kaduna.

An ce a watan Afrilun 2023, ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani shahararren dan kasuwa a kauyen Gangarbi da ke karamar hukumar Rogo ta Jihar Kano, Alhaji Nasiru Na’ayya, tare da kashe mutum daya.

Haka nan a 2021, Masarautar Ƙaraye ta ankarar da cewa masu haƙar ma’adanan Zamfara ba bisa ƙa’ida sun fara shigowa yankin, kuma ta bada shawarin yadda za a magance matsalar.

Kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ci tura domin bai amsa kiran da aka yi masa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
X
DANNA NAN KAGA BIDIYAN 👈😭💣🇳🇪🇳🇬