“Ta Fara Makaranta”: Yarinyar Da Aka Tsinta a Shara Ta Rayu, Ta Zama Kyakkyawa.

Karamar yarinyar da wani ya dauka daga inda aka yasar da ita a Enugu ta rayu kuma har ta fara zama cikakkiyar mutum.

Ben Kingsley Nwashara, ne ya tsinci yarinyar inda ya dunga kula da ita da jin dadinta

Yanzu yarinyar ta fara zuwa makaranta, kuma an wallafa sabon hotonta a Twitterm inda ta tsuma zukata da dama.

Wani matashi dan Najeriya da ya tsinci yarinya a bola watanni da suka gabata ya yi karin haske kan rayuwar yarinyar.

Bawan Allah mai suna, Ben Kingsley Nwashara, ya tsinci yarinyar da wata da ba a san kowacece ba ta yasar sannan ya dunga kula da ita tun daga lokacin.

Yarinyar ta kasance a cikin mugun yanayi lokacin da Kingsley ya tsince ta sannan ya dauke ta zuwa ofishin yan sanda.

Ya bayyana a wata wallafa da ya yi a twitter kwanaki cewa yan sanda basu nuna wani damuwa ba inda suka nemi ya dauke yarinyar daga ofishin yan sandan. Ya ce sai da shugaban yan sandan reshen, DPO ya tsoma baki a wannan rana sannan aka samu maslaha.

Kalamansa:

A yi hakuri da wannan rubutun. Jami’an yan sanda mata uku ne a bakin aiki a ofishin yan sandan da na kai wannan karamar yarinya a wannan daren. Sun fada mani cewa babu abun da za su iya yi mata kuma cewa na tafi da ita. Dukkansu iyaye ne a ganiyar shekarunsu ta 40. Allah ya sakawa DPO din, Bayarabe da na sama washegari da safe, sannan ya umurci daya daga cikin jami’an mata da ta yi mana rakiya zuwa asibitoci daban-daban mun je can tsawon kwanaki uku don haka suka gan shi a matsayin abun gaggawa sannan suka ba mu kulawa yadda ya kamata. Har ma ya ba mu motarsa da direbansa na tsawon kwana 2.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
X
DANNA NAN KAGA BIDIYAN 👈😭💣🇳🇪🇳🇬