Kamfanin Simintin BUA Ya Karya Farashin Siminti Zuwa N3500 Kan Kowani Buhu

Kamfanin BUA ya sanar da rage farashin buhun siminti domin saukaka wa al’ummar Najeriya samun damar yin gine-gine.

Daga ranar Litinin, 2 ga watan Oktoba, buhun simintin BUA zai koma kan farashin N3,500.

Kamfanin ya kuma ce akwai yiwuwar ya sake rage farashin da zarar an kammala aikin sabbin layukan da yake zuwa 2024.

Kamfanin simintin BUA, wanda shine kamfanin siminti mafi girma na biyu a kasuwar Najeriya, ya sanar da rage farashin buhun siminti zuwa N3,500.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X a ranar Lahadi, 1 ga watan Oktoba, kamfanin ya ce sabon farashin zai fara tasiri daga ranar Litinin, 2 ga watan Oktoba.

Farashin buhun siminti a yanzu haka kafin fitar da sanarwar ya kai kimanin N5,000 kowani buhu daya.

Kamfanin BUA wanda yake mallakin attajirin dan kasuwa AbdulSamad Rabiu, ne yana da kayan aiki da ke iya samar da siminti tan miliyan 11.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
X
DANNA NAN KAGA BIDIYAN πŸ‘ˆπŸ˜­πŸ’£πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡¬