An kona wani ɗan ƙungiyar asiri da ake zargi da satar jarirai Guda…

Wasu fusatattun matasa a karamar hukumar Lapai da ke jihar Neja sun kashe wani da ake zargi dan ƙungiyar asiri har lahira.

Wanda ake zargin, mai suna Sani, an kama shi da yara mata guda biyu da ake zargin sace su ya yi a jiya Juma’a.

Wani mazaunin garin mai suna Abdullahi Yahaya ya shaida wa Daily Trust cewa an kama wanda ake zargin da misalin karfe 1:00 na safiya kuma nan take aka kone shi kurmus.

Yayin da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya ce an kona wanda ake zargin kurmus kafin rundunar ‘yan sandan ta isa wurin.

Mista Abiodun ya ce ana zargin wanda ake zargin da satar jarirai a kusa da makabarta a Lapai.

“Da samun bayanan, DPO Lapai ya tattara jami’ai yakums jagoranci tawagar ‘yan sintiri zuwa wurin, amma kafin ‘yan sanda su isa wurin, ’yan bangar da suka fusata dauke da yankan katako da sauran muggan makamai sun yi wa wanda ake zargin duka har kuma suka kona shi.

“An yi kokarin kashe wutar da ceto shi, amma abin takaici, ya kone kurmus, yayin da aka kai gawar zuwa babban asibitin Lapai,” inji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
X
DANNA NAN KAGA BIDIYAN 👈😭💣🇳🇪🇳🇬