Innalillahi: Yakin Nigeria Da Nijar Bazoum Ya Nemi A Kai Masa Dauki.

β€œIna kira ga Amurka da daukacin kasashen duniya, su taimaka wajen maido da doka da oda a Nijar.” Bazoum ya ce cikin makalar da ya rubuta.

WASHINGTON, D.C. β€”
Shugaba Mohamed Bazoum da sojoji suka hambarar da gwamnatinsa a Jamhuriyar Nijar, ya nemi Amurka da sauran kasashen duniya su kai masa dauki.

Cikin wata makala da ya rubuta wacce aka wallafa a jaridar Washington Post, Bazoum mai shekaru 63, ya ce bai ga dalilin da ya sa sojojin suka karbe madafun iko ba.

β€œIna kira ga Amurka da daukacin kasashen duniya, da su taimaka wajen maido da doka da oda. Al’umar Nijar ba za su taba mantawa da taimakon da za ku musu a wannan muhimmin lokaci ba a tarihin kasar.

β€œWannan juyin mulki da wani bangaren sojoji suka yi wa gwamnati a ranar 26 ga watan Yuli ba shi da tushe balle makama.

β€œIdan har suka yi nasara, hakan zai haifar da mummunan sakamako ga Nijar, yankinmu da duniya baki daya.” Bazoum ya ce cikin makalar wacce aka wallafa a ranar Juma’a a jaridar ta Washington Post.

Bazoum ya kara da cewa, babu gaskiya a ikrarin da sojojin suka yi na cewa, tsaron kasar ta Nijar ya tabarbare.

β€œSuna ikirarin cewa yakin da muke yi da masu ikirarin jihadi ba ya nasara, sannan matakan da muke dauka don bunkasa tattalin arzikinmu da sauran tsare-tsare da kawancenmu da Amurka da kasashen turai yana mummunan tasiri akan kasarmu.

β€œHasali ma, tsaro ya inganta a Nijar, kashi 40 na kasafin kudinmu tallafin ne daga kasashen waje, amma hakan ba zai samu ba idan har wannan juyin mulki ya yi nasara.” Bazoum ya ce.

A cewar Bazoum, a kudancin Nijar da ake fama da mayakan Boko Haram, an kwashe shekaru biyu ba tare da an samu wani hari ba, sannan β€˜yan gudun hijira na ta komawa kauyukansu.

Bazoum ya kuma yi gargadin cewa Rasha da sojojin haya na Wagner za su iya yin kaka-gida a yankin idan har juyin mulkin ya dore.

Sojojin da suka yi juyin mulki karkashin Janar Abdourahamane Tchiani, sun ce sun karbe ragamar mulkin kasar ne saboda al’amuran tsaro na tabarbarewa a kasar, sannan matakan da ake dauka don bunkasa fannin tattalin arziki ba sa aiki.

Kasashen duniya da dama sun yi Allah wadai da wannan juyin mulki yayin da kungiyar ECOWAS/CEDEAO, da kungiyar hadin kan Afirka ta AU da ma Majalisar Dinkin Duniya, suke kira da a gaggauta sakin Bazoum tare da mayar da kasar bisa turbar Dimokradiyya.

A makon da ya gabata kungiyar ta ECOWAS/CEDEAO ta kakaba takunkumai akan kasar ta Nijar tare da yin barazanar daukan matakin soja idan masu juyin mulkin suka ki mika wuya.

A ranar Alhamis wata tawagar wakilan ECOWAS/CEDEAO karkashin jagorancin tsohon shugaban mulkin soja a Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar da Sarkin Musulmi Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar III, ta isa Yamai a wani mataki na shiga tsakani a rikicin juyin mulkin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
X
DANNA NAN KAGA BIDIYAN πŸ‘ˆπŸ˜­πŸ’£πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡¬