Dalilin da ya sa na soke lasisin Ali Nuhu, Zango, Gabon, Naziru da sauran ‘yan wasa, furodusoshi da mawaka ‘- Almustapha

Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano, ta ce ta kwace lasisin gudanar da duk wasu ‘yan wasa da jarumai ciki har da daraktoci da furodusoshi a masana’antarta ta shirya fina-finai ta Kannywood.

Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, ya ce matakin na da nufin tsaftace masana’antar da kuma tabbatar da duk wanda ke cikin masana’antar na da cikakkun takardu.

El-Mustapha ya ce dole ne dukkan fitattun jarumai da furodusoshi su sabunta lasisin yin aiki a masana’antar da hukumar.

“Mun soke duk wasu lasisi na duk ƙungiyoyin masana’antar don samun takaddun da suka dace da kuma samun ingantattun tsare-tsare waɗanda za su magance wasu matsalolin da ke cikin masana’antar.

“Muna da kungiyoyi kusan 13, mun kwace dukkan lasisin su, wanda hakan ya ba mu damar tsaftace masana’antar, kafin a ba wa kowane mutum lasisi, dole ne mu gamsu da mutumin.

“Shawarar ta kuma shafi dukkan mawaka da sauran masu nishadantarwa a masana’antar Kannywood;/dole ne su sabunta lasisi, A haka za mu iya tsaftace masna’antar mu gyara shi, sannan mu yi watsi da lalatattu cikin masana’antar.

Sai dai kuma wannan matsayi na Almustapha ya jawo suka daga mutane da dama musamman ‘yan Adawa wadanda suke ganin ana so ayi amfani da siyasa ce kawai domin musguna wa wasu yan fim da basu goyi bayan gwamnati mai ci ba. wato gwamnatin Abba Yusuf na NNPP.

Jarumai irin su Ali Nuhu, Adam Zango da dai sauransu sun yi wa jam’iyyar APC ce aiki a zaben shugaban Kasa da gwamna. Wasu na ganin wannan sabbin dokoki da hukumar ytace finafinan Kano suka kirkiro na da na saba ba haka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
X
DANNA NAN KAGA BIDIYAN 👈😭💣🇳🇪🇳🇬