Anyi Asarar Dukiya Yayin da Gobara Ta Lakume Shugana a Kasuwar Kano.

Fitacciyar kasuwar nan ta jihar Kano ta kama da wuta a daren ranar Laraba, 19 ga watan Yuli.

Gobarar ta kona shaguna 10 kurmus a kasuwar Rimi da ke garin Kano kamar yadda hukumar kwana-kwana ta tabbatar.

Mai magana da yawun hukumar, Saminu Abdullahi, ya ce tartsin wutar lantarki ne ya haddasa gobarar inda ya bukaci yan kasuwa da su dunga kashe kayan wuta idan suka tashi kasuwa.

Jihar Kano – Jami’an hukumar kwana-kwana sun bayyana a ranar Alhamis, 20 ga watan Yuli, cewa gobarar cikin dare ta lakume wasu shaguna a kasuwar Rimi da ke jihar Kano.

Saminu Abdullahi, kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano ya ce shaguna 10 ne suka kone a gobarar wacce ta afku da misalin karfe 8:40 na daren ranar Laraba, 19 ga watan Yuli, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
X
DANNA NAN KAGA BIDIYAN πŸ‘ˆπŸ˜­πŸ’£πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡¬