An Shiga Tashin Hankali Da Jimami Kan Bullar Wata Bakuwar Cuta a Jihar Kaduna.

An samu ษ“ullar wata baฦ™uwar cuta a garin Kafanchan na jihar Kaduna wacce ta salwantar da rayukan mutum huษ—u.

Cutar wacce ba a san kowace iri ba ce dai ta janyo an kulle dukkanin makarantun dake a garin na ganin Kafanchan.

An yi bayanin alamomin cutar tare da kira ga iyaye da sun lura da alamomin a jikin yaransu da su gaggauta zuwa asibiti.

Kafanchan, Jihar Kaduna – Wata baฦ™uwar cuta da ta ษ“ulla a garin Kafanchan, hedkwatar ฦ™aramar hukumar Jama’a a jihar Kaduna, ta yi sanadiyyar salwanyar rayukan mutum.

Jaridar Aminiya ta kuma bayyana cewa ษ“ullar cutar ta sanya an killace wasu mutum 10 a babban asibitin tunawa da Patrick Yakowa da ke a garin na Kafanchan.

ฦullar cutar ta sanya an kulle makarantu a garin na Kafanchan bayan hukumomi sun sallami ษ—alibai ranar Alhamis da safe.

Babban sakataren asibitin, Ezra Joshua, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce tuni har an ษ—auki samfurin cutar domin zuwa yin gwaji domin gano irin cutar a Kaduna.

Ya kuma bayyana cewa sun killace mutum 10 waษ—anda aka kawo musu a tsakanin ranakun Laraba da Alhamis.

Joshua ya yi bayanin cewa cutar tana kama yara ne ฦ™anana masu shekara ษ—aya zuwa 13 inda ta ke yi musu illa ba tare da ษ“ata lokaci ba tana kama su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
X
DANNA NAN KAGA BIDIYAN ๐Ÿ‘ˆ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ’ฃ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ฌ