Miyagun ‘Yan Bindiga Sun Bindige Basarake Har Lahira a Jihar Imo.

Yan bindiga sun halaka Basaraken Nguru da ke ƙaramar hukumar Aboh Mbaise a jihar Imo, Kudu maso Gabashin Najeriya.

Wata majiya ta ce da misalin ƙarfe 3:00 na yammacin ranar Litinin ɗin nan maharan suka shiga har fadar sarkin suka aikata haka.

Hukumar ‘yan sanda ta ce tuni kwamishina ya kafa tawagar kwararrun jami’an da zasu gudanar da bincike kan kisan.

Imo state – ‘Yan bindiga sun harbe basaraken garin Nguru, ƙaramar hukumar Aboh Mbaise a jihar Imo, mai martaba Eze James Nnamdi, har lahira ranar Litinin da yamma.

Jaridar Punch ta tattaro cewa yan bindigan sun kutsa kai har cikin fadar basaraken kuma suka yi ajalinsa da yammacin yau Litinin, 17 ga watan Yuli, 2023.

Rahotanni sun nuna cewa Marigayi sarkin ya karɓi bakuncin wani mai suna, Chief Ignatius Nwaru, yana tsaka da sauraron bakon lokacin da maharan suka kutsa kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
X
DANNA NAN KAGA BIDIYAN 👈😭💣🇳🇪🇳🇬