‘Yan Sanda Sun Tsare Wani Matashi Kan Zargin Sheke Mahaifiyarsa Har Lahira, Ya Na Asibitin Kwakwalwa.

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta ce ta kama wani matashi da ake zargin ya shake wuyan mahaifiyarsa.

Wanda ake zargin Sikiru Samson ya aikata hakan ne a kauyen Itanrin da ke karamar hukumar Ijebu-Ode a cikin jihar Ogun.

Rundunar ta ce yanzu haka Sikiru ya na asibiti bangaren masu ciwon kwakwalwa don duba lafiyarsa.

Jihar Ogun – Wani matashi mai suna Samson Sikiru ya shake wuyar Mahaifiyarsa har lahira a karamar hukumar Ijebu-Ode da ke jihar Ogun.

Matashin wanda ake zargin yana shan kwayoyin maye ya aikata hakan ne a ranar Lahadi 16 ga watan Yuli a kauyen Itanrin.

Kanin wanda ake zargin shi ya tona asiri bayan ya dawo daga aiki ya tarar da mahaifiyar tasu ta mutu.

Vanguard ta tattaro cewa makwabta sun kama Samson tare da mika shi ga ‘yan sanda bayan sun fahimci shi ya kashe mahaifiyarsa.

Yayin tabbatar da faruwar lamarin, mai hulda da jama’a na rundunar a jihar, Omotola Odutola ta ce sun samu labarin kashe matar.

Ta ce yanzu haka Samson na asibiti a bangaren masu ciwon kwakwalwa don ba shi kulawa.

Ta kara da cewa a lokuta da dama ‘yan uwan nasa suna daure shi don kada ya ji wa wani ciwo ko kansa, cewar Channels TV.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
X
DANNA NAN KAGA BIDIYAN πŸ‘ˆπŸ˜­πŸ’£πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡¬