Sojojin Najeriya Sun Kama Babban Mota Makare Da Muggan Makamai Za A Kai Su…

Sojojin Najeriya sun yi nasarar kama wata babbar mota makare da miyagun makamai a jihar Ogun.

An bayyana cewa an shigo da makaman ne daga kasar Mali, yayin da ake shirin kai su jihar Anambra.

Jami’an sojin sun roki ‘yan Najeriya da su cigaba da ba su bayanai kan duk wata barazana ta tsaro da suka lura da ita.

Jami’an bataliya ta 192 ta rundunar sojojin Najeriya, ta damke makamai masu tarin yawa a yayin da ake kokarin kai su jihar Anambra, a ranar Asabar, 15 ga watan Yulin shekarar 2023.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar sojin, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan a shafin Tuwita na rundunar tsaron Najeriya.

Sojojin wadanda suka samu bayanai na sirri, sun tare titin Ajilete zuwa Owode da ke karamar hukumar Yewa ta Arewa ta jihar Ogun, inda suka kama manyan bindigu da tarin albarusai a cikin wata babbar mota mai lamba ENU 697 XY.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
X
DANNA NAN KAGA BIDIYAN 👈😭💣🇳🇪🇳🇬