Miji Ya Yi Barazanar Sakin Matarsa Saboda Ta Ki Daukar Ciki, Don Haifar Masa Da Na Huɗu.

RIkita-rikita yayin da wani dan Najeriya ya yi barazanar sakin matarsa da suka haifi ‘ya’ya hudu.

Mutumin na zargin matar da shan kwayoyin hana daukar ciki bayan ta ki haifa masa da na biyar.

Mutane da dama sun mai da martini inda mafi yawa suke kushe wannan hali na mutumin.

Wani dan Najeriya ya yi barazanar sakin matarsa saboda kin amincewa da kara haihuwa da shi.

Mutumin ya ce matar tasa bayan ta haifi ‘ya’ya hudu ta ce ba za ta sake haihuwar da na biyar ba, cewar Legit.ng.

Wani mai amfani da kafar sada zumunta ta Facebook, Imaan Mike Umoh shi ya wallafa hakan inda ya ce abin ya faru a layin unguwar su.

Ya ce mijin na zargin matar ta na shan kwayoyi don hana ta daukar ciki wanda yanzu haka suna da ‘ya’ya hudu da matar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
X
DANNA NAN KAGA BIDIYAN 👈😭💣🇳🇪🇳🇬