Yan Bindiga Sun Sace Ma’aikatan Titin Hanyar Kaduna-Kano

Mahara da ake kyautata zaton ฦดan bindiga ne sun sace wasu daga cikin ma’aikatan da ke aikin titin hanyar Kaduna-Kano.

ฦณan bindigan dai sun farmaki ma’aikatan ne a gidansu da ke Tashar cikin ฦ™aramar hukumar Makarfi ta jihar Kaduna.

A yayin harin ฦดan bindigan sun yi awon gaba ษ—a mutum huษ—u daga cikin masu aikin yayin da wasu mutum biyu kuma suka samu raunika.

ฦณan bindiga sun yi awon gaba da wasu daga cikin ma’aikatan kamfanin da ke aikin titin hanyar Kaduna zuwa Kano a garin Tashar Yari na ฦ™aramar hukumar Maฦ™arfi a jihar Kaduna.

Jaridar Aminiya ta kawo rahoto cewa wasu daga cikin ma’aikatan mutum biyu sun samu raunika inda ake duba lafiyarsu a asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke a Shika, Zaria.

Maharan dai sun kai harin ne a ranar Asabar.

Wata majiya a yankin ta bayyana cewa maharan sun yi wa gidan da ma’aikatan ke zaune ฦ™awanya ne sannan suka sace mutanen.

Lamarin dai ya auku ne a babban titin Kaduna/Zaria/Kano wanda ma’aikatan na daga cikin masu yin aikin gyaran titin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
X
DANNA NAN KAGA BIDIYAN ๐Ÿ‘ˆ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ’ฃ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ฌ