Matar Da Ta Farfado Ana Shirin Kaita Makwanci Ta Sheka Da Gaske.

Wata mata ‘yar ƙasar Ecuador, Bella Montoya, ta farka a cikin akwatin gawarta a lokacin da ake shirin kai ta makwanci.

A ranar 9 ga watan Yuni ne aka ayyana bisa kuskure cewa Montoya ta rasu, wacce ana ƙoƙarin kai ta makwanci ne ta farfaɗo.

An ajiye Montoya a asibiti bayan faruwar lamarin, sai dai kuma abin takaici, ta mutu sakamakon bugun jini a ranar Juma’ar da ta gabata.

Bidiyon wata tsohuwa ‘yar ƙasar Ecuador da ta farfaɗo bayan sanyata cikin akwatin gawa ya karaɗe kafen sada zumunta a makon da ya gabata.

Sai dai hukumomi a ranar Lahadi, sun sanar da cewa, matar ta mutu daga baya, kamar yadda The Punch ta wallafa.

A cikin wani dan gajeren bidiyo da ya yaɗu a shafukan sada zumunta a makon da ya gabata, an ga matar mai suna Bella Montoya, ‘yar shekara 76, a cikin buɗaɗɗen akwatin gawarta tana numfashi sosai yayin da wasu maza biyu ke ƙoƙarin taimaka ma ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
X
DANNA NAN KAGA BIDIYAN 👈😭💣🇳🇪🇳🇬