innalillahi Yan Bindiga Sun Hallaka Wani Dan Shekara 13 Baya Sunyiwa…

Tashin Hankali Yayin da Tsageru Suka Bindige Wani Yaro Dan Shekara 13 Tare da Sace an Sace Wani a Bauchi.

Rahoton da muke samu daga jihar Bauchi ya bayyana yadda aka harbe wani yaro a kasuwar Jama’are.

An kuma tattaro yadda ‘yan bindigan suka sace wani mutum a harin da suka kai ranar kasuwar mako.

Ya zuwa yanzu, ‘yan sanda sun labarta yadda lamarin ya faru da kuma irin matakin da suka dauka.

Jihar Bauchi – Wasu ‘yan bindiga da suka kai hari kasuwar Jama’are da ke jihar Bauchi sun harbe wani yaro mai suna Khalifa Umar mai shekaru 13 har lahira.

Rahoton da muka samo daga gidan talabijin na Channels ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun kuma yi garkuwa da wani Alhaji Sama’ila Magaji tare da raunata wasu mutum biyu a daren ranar Asabar.

Wani mazaunin garin Jama’are ya ce mutane sun yi mamakin harin domin sabon abu ne a gare su kuma Jama’are ba ta da dazuzzukan da ke kusa da jama’a.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Ahmed Wakili ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi 18 ga watan Yuni.

A cewar Wakili ga Channels:

“Jiya, da misalin karfe 20:10:00 wato misalin karfe 8:10 na yamma wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun zo da yawa a kan babura.

“Sun mamaye kasuwar Jama’are suna harbin iska inda suka yi garkuwa da wani Alhaji Sama’ila Magaji, suka harbe wani Khalifa Umar mai shekaru 13 sannan suka raunata wani Mustafa Sabiu dan shekara 51 kana suka harbe shi a cinyarsa. Harsashin ya kuma gogi wani daga mai suna Rapheal na Chiboke a cikinsa.”

Bayan samun labari, rundunar ‘yan sandan ta tura jami’ai domin kai dauki ga mazauna da wadanda suka zo cin kasuwar.

Ya bayyana cewa jami’an ‘yan sanda sun je wurin da lamarin ya faru, inda suka ceto wanda ya jikkata kana suka zarce da shi asibiti.

A wajen da aikin ta’addancin ya faru, an gano kwanson harsasai guda hudu na AK 47, an kuma samu harsashin da ba a harba ba guda daya.

An tattaro cewa an ba da gawar wanda aka kashe ga iyalan don yi masa jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Ya zuwa yanzu dai jami’ai sun bazama domin tabbatar da tsaro da neman inda aka kai wanda aka sacen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
X
DANNA NAN KAGA BIDIYAN 👈😭💣🇳🇪🇳🇬