Bidiyon Kama Daloli A Gidan Emefiele Gaskiya Ta Fito Jibi Yadda…

Rundunar β€˜yan sandan sirri ta Najeriya ta kama gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.

Kwanaki kadan, wani faifan bidiyo ya rika yawo a wasu kafafen sada zumunta, ciki har da WhatsApp, inda ake cewa an samu kudi a gidan Emefiele.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Emefiele a ranar Juma’a, 9 ga watan Yuni, 2023, biyo bayan binciken da ake yi a ofishinsa.

Wani faifan bidiyo mai tsawon dakika 27 wanda ya yadu a kafar sada zumunta ya nuna wasu mutane biyu suna shirya makudan kudade suna kirga su da inji.

Wadanda suka yada bidiyon sun yi nuni da cewa, hukumar DSS ce ta gano wasu makudan kudade a gidan Godwin Emefiele, korarren gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).

Jaridar Legit.ng ta lura cewa galibin wadanda ke yawo da bidiyon magoya bayan shugaba Bola Tinubu ne – kamar yadda ya bayyana a nan da kuma nan.

Hakanan, bidiyon wanda ke nuna alamar kudaden dalar Amurka ba shi da sauti.

Jaridar The Cable a cikin bincikenta da ta buga a ranar Juma’a, 16 ga Yuni, ta ce faifan bidiyon ya samo asali ne daga kasar Sudan, wata kasa a Arewacin Afirka.

Bin diddigi ya ce, an sake bidiyon ne a ranar 22 ga Afrilu, 2019, lokacin da aka gano wani babban tafkin kudi – wanda ya kai dalar Amurka miliyan 7 – a gidan Omar Bashir, hambararren shugaban kasar Sudan, inji rahoton Arab News.

A halin yanzu, Bashir yana Asibitin Aliyaa, Omdurman, bayan fitowa daga gidan yari a wani kazamin fada da aka gwabza a kasar.

Tsohon shugaban dan shekaru 79, wanda ya mulki Sudan tsawon shekaru 30, an hambarar da shi ne a wani boren β€˜yan tabare da ya barke a shekarar 2019.

Hakazalika, Peter Afunaya, mai magana da yawun hukumar DSS, ya bayyana cewa faifan bidiyon da ake alakantawa da Emefiele β€œkarya ne”.

Ya bayyana hakan ne a wata fusatacciyar sanarwar martani ga bukatar da aka yi ya ba da bayani game da bidiyon.

Yanzu dai ana bincike kan Emefiele, kuma ana ganin kamar akwai matsalolin kudi da suka shafi kujerar da ya bari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
X
DANNA NAN KAGA BIDIYAN πŸ‘ˆπŸ˜­πŸ’£πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡¬