Rikici ya Barke Tsakanin Sojoji da ‘Yan Sanda, an Sheke ’Yan Sanda Biyu A Ofishin hukumar INEC.

Rikici ya Barke Tsakanin Sojoji da ‘Yan Sanda, an Sheke ’Yan Sanda Biyu A Ofishin hukumar INEC.

An hallaka jami’an ‘yan sanda biyu an kuma jikkata biyu yayin da fada ta barkewa tsakaninsu da sojoji a Jalingo da ke jihar Taraba a ranar Litinin.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa, an samu sabani ne tsakanin ‘yan sanda da sojoji a hedkwatar hukumar zabe ta INEC, lamarin da bai zo da dadi ba.

Danna Hoton nan 👆👆👆

A cewar majiya, sojojin sun kori dukkan jami’an ‘yan sandan da ke bakin aiki ne a ofishin tattara sakamakon zaben jihar da ke hedkwatar INEC.

‘Yan sandan da suka samu rauni a halin yanzu an kai su asibitin tarayya da ke birnin Jalingo, kamar yadda majiyoyi daga jihar suka shaida, Daily Trust ta ruwaito.

An ruwaito cewa, an lalata motocin da ke ajiye a cikin hedkwatar ta INEC a lokacin da rikicin ya yi kamari.

An kuma yi harbe-harbe da ya jawo tashin hankali ga mazauna yankin, har ta kai aka rufe shagunan da ke zagayen wurin.

A tattaunawa da manema labarai, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Sulaiman Amodu ya ce, an shirya tawagar bincike mai zurfi don gano tushen lamarin.

Tattaunawar da kwamishinan ya jagoranta ta hada da kwamandan sojin Najeriya a Brigade 6 da ke Jalingo, Br. Janar Frank Etim da kuma daraktan hukumar DSS a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
X
DANNA NAN KAGA BIDIYAN 👈😭💣🇳🇪🇳🇬