Da Dumidumi: Zaɓen Najeriya 2023: Jennifer Efidi, yadda aka ji min ciwo a fuska a wajen zaɓe.

Da Dumidumi: “Na je rumfar zaɓena, na tarar da dogon layi, ni ma na shiga layin, na ga sunana. Sai na koma gefe na zauna ina jira a zo kai na. Kawai sai na ji ƙarar bindiga.”

Danna wannan Hoton⬆️

Yadda Madam Jennifer Efidi ta yi bayani ke nan kan abin da ya faru da ita lokacin da ta je zaɓen shugaban ƙasa da na majlisar dokoki a ranar Asabar.

Hotunan Madam Bina jennifer Efidi da idonta ɗaya a toshe da kuma ɗinki a fuskarta a rumfar da ta yi zaɓe a Legas, lokacin da take kaɗa ƙuri’arta sun karaɗe kafofin sada zumunta a ƙarshen mako.


Mutane da dama sun rinƙa jinjina wa kwarin gwiwarta da jajircewarta kan yadda ta koma domin kaɗa ƙuri’arta duk da irin raunin da ke fuskarta.


A wannan tattaunawar da ta yi da BBC ta bayyana yadda lamarin ya faru, da kuma abin da ya sa ta koma domin kaɗa ƙuri’arta duk da cewa an jikkata ta.

‘Na ji ƙarar bindiga’

Efidi ta ce, ba ta taɓa zaton za ta samu kanta a cikin irin wannan yanayi ba a rumfar zaɓenta wadda ba ta da nisa da gidanta, ganin cewa a baya ba su taɓa fuskantar tashin hankali ba a mazaɓar.

“Na je mazaɓata, na samu dogon layi, don haka na shiga layin, bayan na duba sunana, sai na samu waje na zauna ina jiran layi ya zo kaina.

“Bayan wani lokaci, sai wasu yara suka zo inda muka yi layi, a lokacin ana ci gaba da zaɓe cikin lumana.”

“Bayan kamar minti 30, sai na ji kamar wani abu ya daki fuskata kamar an jefe ni da wani abu. Kawai sai na ji ƙarar bindiga na tashi, na yi tunanin sun harbe ni. Jama’a sun ringa gudun ceton rai, sai na taɓa fuskata kawai sai na ji jini yana zuba a hannuna. Sai na fara ihun neman ɗauki, amma mutane guduwa kawai suke yi suna ta kan su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
X
DANNA NAN KAGA BIDIYAN 👈😭💣🇳🇪🇳🇬